Ƙetare
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sake sanya dokoki masu tsauri ga yan Najeriya

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE ta sake saka wasu dokoki masu tsauri ga ‘yan kasar nan da ke neman bizar shiga ƙasarta domin yawon buɗe ido ko ziyarar wucin-gadi.
Sanarwar da ƙasar ta fitar ta haramta bai wa ‘yan Najeriya bizar wucin-gadi, kuma ɗuk wani ɗan Najeriya mai shekaru 18 zuwa 45 ba za a ba shi bizar shiga ƙasar ba, sai tafiyar ta kasance da iyali.
Sabon matakin na zuwa ne kusan shekara ɗaya da UAE da Najeriya suka shawo kan matsalar haramcin bizar na shekara biyu da aka kakabawa ‘yan Najeriyar.
A yanzu dai wannan sabon doka na nufin an soke ba wa ‘yan Najeriya bizar wucin-gadi baki daya haka zalika ga wanda ya haura shekara 45 idan yana neman biza sai ya gabatar da takardar bayanan asusun ajiyar sa na banki na tsawon wata shida, wanda zai nuna yana da kuɗaɗen da suka kai dala dubu 10 a lokacin neman bizar.
Sai kuma bukatar gabatar da Otel din da mutum zai yi masauki da kuma wasu bayanai na fasfo.
You must be logged in to post a comment Login