Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Haƙiƙanin abin da ke faruwa tsakanin KAROTA da Ƴan Adaidaita

Published

on

Dambarwar tsakanin hukumar KAROTA da kuma masu baburan adaidaita sahu ba sabon abu bane, hassalima dama an saba karan batta a tsakaninsu.

Wane haraji KAROTA ta sanya wa ƴan adaidaita sahu?
KAROTA ta sanya wa masu baburan biyan harajin Naira ɗari-ɗari a kullum.

A wata hira da shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba, ya yi a kafafen yaɗa labarai ya ce, biyan harajin ba sabon abu ba ne, daman akwai shi a cikin doka.

Me ya sa masu adaidaita basu amince da biyan harajin ba?
Mafi yawan masu adaidaita sahu da Freedom Radio ta zanta da su, sun amince da biyan harajin, ba su da jayayya a kai.

Mene ne ƙorafin masu adaidaitar?
Mafi akasari suna ƙorafi ne kan hanyar da hukumar ta fitar domin biyan kuɗin.

KAROTA ta ɓullo da tsarin biyan Naira ɗari ɗin amma ta banki, ko kuma a shagunan intanet wato Cafe.

Wasu Ƴan adaidaita sun shaida wa Freedom Radio cewa, in suka je biya, sai a nemi su biya Naira ɗari biyar kuɗin Remita, sannan su biya mai Cafe kuɗin aikin da ya yi musu.

Jimilla dai suna biyan kuɗi har kimanin dubu guda kafin samun biyan kuɗin.

Sannan akwai cunkoso a shagunan intanet ɗin, wasu lokutan kuma in sun je babu Network

Kuma ance kullum sai ka biya wannan kuɗi sannan zaka hau titi.

Masu adaidaitar suka ce, idan suka dunƙule suka biya na wata biyu, da KAROTA ta ce, suna iya biya domin su huta.

To amma bayan sun biya, sai a ce musu ai na watan Janairu da Fabrairu suka biya, kaga kenan mako mai zuwa za a shiga sabon lissafi.

Meye hanzarin KAROTA kan wannan batun?
Da yake martani a hirar sa ta kafafen yaɗa labarai, Baffa Babba ya ce, sun fitar da tsarin biyan kuɗin ta banki da Remita saboda gudun masu cuwa-cuwa.

Ya ce, kuma hakan shi ne mafi sauƙi domin basu da ma’aikatan masu yawan da za su iya karɓar kuɗin harajin ya zama kowa ya biya cikin kowace rana sai ta wannan hanyar.

Baya ga haka, Baffan ya ce, sun ma samar da manhaja ta wayar hannu, ta yadda masu adaidaitar za su iya biyan kuɗin ta wayarsu nan take.

Labarai masu alaka:

 Zamu sasanta rikicin KAROTA da ‘Yan adaidata sahu – NLC

Babu sassauci ga ƴan adaidaitar da ba sa biyan haraji – KAROTA

Ƴan adaidaita sahu na zargin shugabanninsu sun zama ƴan amshin shatan KAROTA

Mafi yawa daga cikin masu adaidaita sahun da muka zanta da su, sun nuna fargabarsu kan jagororin su.

A cewar su, shugabannin ba sa kare muradansu maimakon hakan sun koma ƴan abi yarima asha kiɗa, suna mara wa KAROTA baya.

Sai dai shugabannin sun sha musanta wannan zargi tare da cewa, suna yin iya ƙoƙarin su domin tabbatar da maslaha da daidaito a tsakani.

Wannan dai su ne jigon abin da ya haifar da tsunduma yajin aikin ranar Litinin da ƴan adaidaita suka yi, wanda kuma wasu abubuwan ke fitowa a cikinsa wanda suka haɗa da yunƙurin Gwamnatin Kano na maye gurbin su, la’akari da furucin da shugaban hukumar ya yi na cewa, sun fi so ma a daina sana’ar

Labarai masu alaka:

Gwamnati ta soke adaidaita ko a yi musu garambawul – Baffa Babba

Biyan haraji ya zama dole – Saƙon Baffa ga ƴan adaidaita

Masana shari’a na da hanzari
Masana shari’a irinsu Barista Abba Hikima Fagge ya bayyana matakin an KAROTA a matsayin abin takaici.

Barista Fagge ya ce, matakin na KAROTA ga ƴan adaidaita ya saɓa da doka, kuma idan za a yi irin wannan ba abu ne da ya kamata a yi shi da ka kawai ba.

Ku ci gaba da bibiyar Muryar Jama’a domin jin inda aka kwana aka tashi kan wannan batu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!