Labarai
Haɗin kan al’umma ne ke samar da ƙasa ɗaya dunƙulalliya – Dakta Sa’idu Dukawa
Shugaban sashin nazarin harkokin mulki da gudanarwa a jami’ar Bayero kuma masanin kimiyyar siyasa a nan Kano ya ce, ƙasa ɗaya dunƙulalliya na samuwa ta hanyar haɗin kan al’ummar da ke rayuwa a cikin ta.
Dakta Sa’’idu Ahmad Dukawa ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.
Dukawa ya ce “Kasa a siyasance na nufin wani guri da al’umma da yawa ke zaune kuma yaruka daban-daban ɗabi’unsu daban, al’adunsu daban, amma suna zaune tare kuma suna rayuwa tare cikin kwanciyar hankali”.
“Gwamnati ita ce akan gaba wajen haɗa kan ƙasa, ta hanyar samarwa da al’ummar da ta ke mulka ilimi, lafiya da kuma yin adalci” in ji Dukawa.
Masanin ya kuma ce, in dai ana so ƙasa ta zama ɗaya dunƙulalliya to kuwa sai shugaban da ya ke jagorantar ta ya sauke nauyin da ke kan sa.
Da kuma tuna cewa al’ummar su ne suka zaɓe shi don ya jagorance su.
You must be logged in to post a comment Login