Labarai
Hadin kan Gwamnatin tarayyar ga manoma zai bunkasa noma- Sarkin Kano
Mai martaba Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga gwamnatin tarayya kan ta bai wa manoma hadin kai wajen samar musu kayayyakin noma na zamani domin samar da wadataccen abinci a Nijeriya.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara gidan gonar Malam Alu da ke birnin kudu ta jihar Jigawa.
Sarkin ya ce, gidan gonar Babu irinsa a arewacin Nijeriya duba da irin noman Tumatir da kiwon shanu da kaji da kuma samar da Madarar Shanu mai inganci da ake yi a gonar.
A nasa jawabin mai martaba sarkin Dutse Alhaji Muhammadu Hamim Nuhu Sunusi ya ce, ‘sun ji dadin wannan ziyara da sarkin kano ya kai musu.
Mai martaba sarkin kano yayin ziyarar ya na tare da hakimansa.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login