Kiwon Lafiya
Hadurra 196 da suka afku bana a Najeriya sun janyo asarar dukiyoyin kusan biliyan 10
Hukumar kiyaye abkwaur hadurra ta kasa (FRSC), ta ce hadurra guda dari da casa’in da shida da suka wakana a cikin kasar nan a wannan shekara sun yi sanadiyar asarar dukiyoyi na kusan biliyan goma.
Shugaban hukumar na kasa Boboye Oyeyemi ne ya bayyana haka yayin wani taron karawa juna sani da kungiyar NUPENG ta shirya wa direbobin tankokin dakon mai a Lagos.
Ya ce asarar ta shafi rasa rayuka da ababen hawa da dukiyoyi da ma kansu hanyoyin da ake yin hadurran a kansu.
Sai dai ya ce duk da haka an samu raguwar hadurra da asarar, idan aka kwatanta da wa’adi irin wannan a shekarar da ta gabata.
Shugaban hukumar ta FRSC ya kuma ce a wa’adi irin wannan a shekarar 2016 hukumar ta tattara kididdigar hadurra 282 yayin da a shekarar 2017 aka samu hadurra 240.