Labarai
Hakkin ‘yan Fansho: Majalisar dokokin Kano za ta yi bincike
Majalisar dokokin jihar Kano ta ce za ta gudanar da bincike kan hakkokin yan fansho na Kano.
A cewar majalisar za ta ɓullo da hanyoyin da za su sauƙaƙa wa ƴan fansho samun haƙƙoƙinsu yadda ya kamata.
Shugaban kwamitin harkokin fansho na majalisar kuma shugaban masu rinjaye Alhaji Labaran Abdul Madari ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kwamitin amintattu na ƴan fansho ya kammala kare kasafinsa na baɗi.
Ya ce, daga tattaunawar da kwamitinsa ya yi da shugabancin kwamitin amintattun ƴan fansho sun gano cewa akwai buƙatar ƙara yin nazari tare da lalubo hanyoyin kawo gyara a fannin.
Yanzu haka dai kusan dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar Kano sun kammala kare ƙunshi kasafin nasu na baɗi.
You must be logged in to post a comment Login