Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Halin da aka wayi gari a wasu sassan Kano

Published

on

Wasu masu bibiyar Freedom Radio kenan suka aiko da saƙon yadda aka wayi gari yau Talata 25-08-2020 a yankunan su.

S Kwayo Sauna Kawaji

“a gaskiya mu dai a nan unguwar Sauna Kawaji, mun tashi lafiya, ga kowa nan ya fito bakin neman sa ana al’amura da hada-hada cikin jin daɗi da annushuwa.

Alhamzat Shoe

Barkanku dai gaba ɗaya ma’aikatan Freedom Radio mun tashi lafiya a nan yankin Hotoro NNPC Mega jama’a dai an fara fitowa wajen harkokin yau da kullum.
Muna fatan Allah yabawa kowa rabonsa na alheri.

Nura Mu’azu Bilya

Barkanku da safiya a yankinmu na Zangon Dakata mutane sun tashi cikin koshin lafiya kuma kowa yana kokawar fita neman abin da zai rufawa kansa asiri musamman ma ƴan adaidaita sahu gashi nan sun cika tituna.

Sulaiman Bala Mai Ruwa

Slm daga bakin kasuwar Gama bayan Mini Stadium yanzu haka dai ƴan kasuwa sun fara buɗe shaguna don fara kasuwanci kamar yadda aka saba.

Mubarak Musa Ataya

Daga nan unguwar Ƙofar Waika komai lafiya yake wakana muna fatan dai Allah ya ƙara zaunar mana da ƙasar mu lafiya.

Hussain Musa Jodaɗe

Daga Garin Jodaɗe ƙaramar hukumar Ƙunchi abin da ke faruwa muna fama da Tsuntsaye masu jan Baki suna cinye mana Gero dan Allah ayi mana kira ga gwamnati ta kawo mana ɗauki.

Adamu Ɗanjuma Muhammad

Daga Indabo, ƙaramar hukumar Wudil, Mash Allah komai lafiya kowa ya fito yana harkokinsa, Sai dai godiya ga Allah da fatan ya ƙara bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wasilu Auwalu Ayagi

To cikin Ikon Allah mun wayi gari lafiya daga nan Unguwar Aisami sai dai an sami rushewar wasu Gidaje cikin Ikon Allah kuma abin mamaki kusan duk a tare sakamakon ruwan jiya don haka a ƙara jan hankalin mutane a ƙara kulawa da Garuka wadanda za a riƙa tsayawa kusa da su.

Magaji Bangiss Ƴanbarka daga ƙaramar hukumar Kumbotso
A yankin mu na garin Ƴanbarka muna fama da rushe-rushen muhalli sakamakon ruwan sama da ake yi mai yawan gaske.

Da fatan Allah ya bamu wucewa damu lafiya.

Fiddausi Ibrahim Na’ibawa

Haƙiƙa unguwar mu ta Na’ibawa har zuwa Unguwar Ƴanlemo kowa ya tashi lafiya, sai dai zaizayar ƙasa da babban layin Chairman yake fama da shi, inda mukayi kira ga mahukunta amma har yanzu shiru muke ji.

Shiga Facebook domin ci gaba da karanta sakonnin:

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!