Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Har yanzu bamu farfaɗo daga illar annobar Corona ba – Ƙungiyar masu dabino

Published

on

Ƙungiyar masu sana’ar sayar da dabino ta ƙasa ta ce, har yanzu ba su farfaɗo daga illar da annobar corona ta yi sana’ar su ba.

Shugaban ƙungiyar na Kano Alhaji Auwalu Ɗanbatta ne ya bayyana haka a yayin zantawar sa tashar Freedom Rediyo.

Alhaji Auwal ya ce, tun bayan ɓullar annobar Corona sana’ar ta su ta shiga wani hali a sakamakon a sarar maƙudan kuɗaɗe da suka yi.

“Duk da cewa akwai ɓangarorin kasuwanci da dama a jihar Kano dama kasa baki ɗaya da annobar ta tagayyara su, amma masu sana’ar sayar da dabino abin na su nada matukar ban tausayi da kuma damuwa” a cewar Alhaji Auwal.

“Dalilin da yasa na faɗi haka kuwa shi ne, yadda mutane da dama suka karɓi ƙayan kuma basu da kuɗin biya, sannan kuma ga asarar da masu sayarwar suka tafka dalilin dokar kulle wadda a yanzu suna fuskantar barazanar gurfanarwa a gaban kotu daga wajen waɗanda suke karɓar kayan”.

Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati a dukkanin matakai da su tallafawa masu sana’ar sayar da dabino kamar yadda suke tallafawa sauran ɓangarorin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!