Coronavirus
Har yanzu cutar Corona tana nan inji likitoci
Kungiyar likitoci ta kasa, ta yi kiga ga al’umma da su kasance masu bin ka’idojin da hukumomin lafiya suka bayar kan cutar corona, kasancewar har yanzu cutar na nan.
Shugabna kungiyar na kasa mista Inoocent Ujah ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin tarraya Abuja.
Mista Innocent Ujah ya ce, wannan lokaci ne da ya kamata al’umma su rubanya kokari wajen amfani da matakan kariya a wani bangare na rage yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
Yana mai cewa, al’umma su yi watsi da zancen nan na cewa, cutar Corona ta tafi, ko kuma babu ma cutar baki daya.
Rahotanni sun ce, ya zuwa yanzu kasar nan na da mutane masu dauke da cutar sama da dubu Ashirin, a inda jihar Kano ke da mutane masu dauke da ita, kimanin dubu daya da dari biyu da Ashirin da Bakwai.
You must be logged in to post a comment Login