Labarai
Har yanzu PDP na nan da ƙarfinta- Abubakar Bukola Saraki

Tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP na nan da ƙarfinta duk kuwa da ƙalubalen da take fuskanta.
Saraki ya ce PDP har yanzu tana da farin jini a faɗin ƙasar nan, inda ya bayyana ta a matsayin jam’iyya da ta shiga ko ina wato kusan kowa ya santa, kuma har yanzu tana da karɓuwa a idon masu kaɗa ƙuri’a a cewar sa.
Ya ƙara da cewa duk da matsalolin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta, PDP na da damar sake farfaɗowa tare da taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya nan gaba.
A cewarsa, abin da ya rage shi ne haɗin kai da kuma gyaran cikin gida domin jam’iyyar ta ci gaba da jan ragamar adawa a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login