Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hatsarin jirgin kasa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 36

Published

on

Akalla mutane talatin da shida ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani hatsarin jirgin kasa da ya abku a kasar Taiwan.

Rahotanni sun ce, hatsarin ya faru ne bayan da jirgin kasar ya kaucewa hanyar sa a gabashin kasar Taiwan da safiyar juma’a.

Bayanai sun ce wannan hatsari shine mafi muni cikin shekaru arba’in da ya gabata a kasar ta Taiwan.

Ministan sifiri da sadarwa na kasar Lin Chia-lung, ya ce, tuni aka kai wasu mutane arba’in wadanda suka jikkata zuwa asibiti don ci gaba da duba lafiyar su.

A bangare guda, masu aikin ceto na ci gaba da zakulo mutane da ake zargin sun makale sanadiyar hatsarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!