Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hatsarin Mota: Ana fargabar liman da matasan Kano 7 sun rasu a Katsina

Published

on

Ana fargabar hatsarin mota a Katsina ya hallaka liman da wasu matasa kimanin bakwai ƴan unguwar Kurna ta jihar Kano.

Mai unguwar Kurna Tudun Bojuwa, Kwaciri Malam Umar Usman ya tabbatar wa da Freedom Radio faruwar al’amarin.

Sai dai yace, har yanzu ba a gama tantance adadin waɗanda abin ya shafa ba.

Matasan unguwar sun gamu da wannan hatsari ne ranar Laraba, a hanyar su ta zuwa jihar Katsina domin ɗaurin auren almajirin babban limamin yankin Malam Iliyasu Nagurasu, wanda shi ma ya rasa ransa a hatsarin.

Freedom Radio ta ziyarci gidan limamin da misalin ƙarfe 4:45 inda ake shirin yi masa jana’iza.

Yanzu haka dai ana zaman alhini a unguwar yayin da ake dakon isowar gawar sauran waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!