Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bamu gayyaci Shatou Garko da iyayenta ba – Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta musanta rahoton cewa ta gayyaci Sarauniyar Kyau Shatou Garko da iyayenta.

Babban Daraktan Hukumar Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

Yace, ba su gayyaci Shatou da iyayenta ba, tambaya ce kawai aka yiwa Kwamandan hukumar Malam Haruna Ibn Sina shi kuma ya yi nasiha.

Babu wani umarni da muka bayar na a gayyato ta ko iyayenta, labari ne na ƙanzon kurege, a cewarsa.

Hisbah ta yi nasiha ne kan bayyana tsiraici wanda haramun ne.

A makon da ya gabata ne aka zaɓi Shatou Garko a matsayin sarauniyar kyau a wani taro da aka yi a birnin Legas.

Sai dai wannan zaɓe ya samu martani daga al’umma kasancewar ita ce ƴar Kano ta farko da ta taɓa samun wannan matsayi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!