Labarai
Hisbah: Mun bada wa’adin mako 2 ga masu aikata baɗala domin tuba
Babban kwamandan Hisbah Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya koma ofishinsa domin ci gaba da aiki bayan ɗinke barakar ta kunno kai tsakaninsa da Gwamnatin kano.
Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan jihar Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya jagoranci raka shugaban hukumar Malan Aminu Daurawa.
Yayin shigar shi ofishin Malam Aminu Ibrahim daurawa ya ce wannan ɓaraka da ta kunno kai tsakanin sa da gwamnatin Kano wasu mutane ne da basa son ci gaban kano suka ƙirƙire ta domin mayar da kano koma baya.
Haka zaliha yace yanzu haka an ɗinke duk wata ɓaraka da aka samu tsakani wanda hakan ya ƙarawa hukumar ƙaimi wajen ci gaba da gudanar da aikin su ka’in da na’in.
Daura ya ce duk wasu mutane da suka san suna aikata baɗala to hukumar ta basu wa’adin mako 2 domin tuba in ba haka ba duk wanda suka kama to dole doka tayi aiki akan sa.
Da yake jawabi Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa yace wannan sasancin da akayi zai kawo karshen baɗala a jihar Kano.
A nasa ɓangaren farfesa Muhammad Babangida da ya kasance guda cikin wa’inda suka shiga zaƙanin sasancin yace wannan sasancin da akayi ba ƙaramin ɗaga darajar Kano zaiyi ba.
Haka zalika an buƙaci al’ummar jihar kano dama ƙasa baki ɗaya da su kasance masu sanya idanu wajen kan tarbiyyar ƴaƴan su domin samun al’umma na gari da ciyar da kano gaba
You must be logged in to post a comment Login