Labarai
Hisbah: Sakamakon binciken ɗan Hisbar da ƴan sanda suka kama a Otal
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ƴan sanda sun karɓe binciken da ta fara kan jami’inta da aka samu a wani Otal da ke Sabon Gari da matar aure.
Babban Kwamandan rundunar Malam Muhammad Haruna Ibn Sina ya shaida wa Freedom Radio cewa, dama ƴan sanda suka cafke shi suka kuma miƙa shi hannunsu daga baya kuma suka karɓe binciken.
A nata ɓangaren rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta tabbatar da hakan.
Baɗala: An cafke babban jami’in Hisbah da matar aure a Otel
Mun karbi korafe-korafe fiye da kowanne lokaci daga farkon shekara nan – Hisbah
Kiyawan ya ce, sun cafke ɗan Hisbar nan bayan da suka samu rahoton motsin da ba su gamsu da shi ba.
Amma daga bisani sun yi bincike sun kuma gamsu da motsin ɗan Hisbar a Otal ɗin.
Kiyawa ya ci gaba da cewa, mutumin ya yi ƙoƙarin taimaka wa matar ne.
Sai dai a wata hira da Freedom Radio ta yi da ɗan Hisbar ya ce, shi ya biya kuɗi har Naira 3,000 ga wani abokinsa wanda shi kuma ya kai ta Otal ɗin.
Daga baya ne shi kuma ya je Otal ɗin ya same ta ya kuma faɗa mata cewa duk wanda ya zo kada ta buɗe ƙofa, daga nan ne sai ƴan sanda suka zo a cewar sa.
DSP. Kiyawa ya ce, suna ƙoƙarin ganin an samu daidaito a tsakanin ɓangarorin da al’amarin ya shafa.
You must be logged in to post a comment Login