Addini
Hisbah ta gano kudade har sama da Naira miliyan 76 a shekara
Sashen kula da manyan laifuka na hukumar Hisbah ta jihar Kano (ICD) ya ce daga farkon watan Janairu zuwa watan Disambar shekara ta 2019 da muke ciki ya kwato kudade kimanin Naira miliyan saba’in da shida N76,000,000 da aka tauyewa jama’a hakki.
Cikin wata sanarwa da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Lahadi ta bayyana cewa hukumar ta samu nasarar kwato kudaden ne biyo bayan korafe-korafen da jama’a suka shigar a gabanta kan zargin tauye musu hakki.
Wanda hukumar Hisbar ta bibiya har aka samu karbo zunzurutun kudi har miliyan ashirin da shida da dubu dari biyar da arba’in da bakwai da dari bakwai da biyar N26,547,705.
Kazalika anyi yarjejiniya da wadanda akai korafi akansu kan zasu biya kudaden da ake binsu wanda ya kai har sama da naira miliyan talatin da tara N39,000,000, wanda izuwa yanzu tuni suka cigaba da kawo kudin lokaci zuwa lokaci ga hukumar Hisban, kuma tana mikasu ga masu su.
Sanarwar ta kara da cewa sashen manyan laifuka na Hisbah ya karbi korafe-korafe har guda dubu biyu da dari hudu da sittin da biyu 2462 inda ta samu nasarar kammala dubu daya da dari biyar da arba’in da daya sauran kuma ta turasu zuwa inda ya dace.
Labarai masu alaka:
Hisbah bata da hurumin yin bulala ko cin tara ga mai laifi -Barista Sunusi Musa
Hisbah ta shirya cafke masu hada mata da maza a adai-daita sahu