Labarai
Hisbah ta shirya cafke masu hada mata da maza a adai-daita sahu
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce daga ranar daya ga watan Janairu na sabuwar shekara mai kamawa za’a daina cakuduwa tsakanin maza da mata a Babura masu kafa uku na adai-daita Sahu.
Abdullahi Umar Ganduje bayyana hakan ne ta bakin kwamandan hukumar hisba na jihar Kano Sheikh Muhammad Harun Ibin Sina yayin taron kungiyar dalibai musulmi ta kasa da ya gudana yau a jami’ar Bayero.
Harun Ibini Sina ya ce duk direban baburin adai-daita sahun da aka kama na hada maza da mata daga ranar daya ga watan na janairu to babu shakka zai fuskanci hukunci mai tsauri.
Da yake jawabi yayin taron sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na biyu ja hankalin matasa da dalibai kan su rika taimakawa wajen bunkasa habakar tattalin arzikin Najeriya, wanda ta hakan ne kawai za’a iya magance matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a kasar nan.
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya rawaito cewa yayin taron mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya ja hankalin al’umma kan su dinga taimakawa jami’an tsaron kasar nan don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Labarai masu alaka:
Hisba ta yi karin girma ga manyan jami’anta