Kiwon Lafiya
Hukumar aikin hajji ta kasa ta fitar da wasu lambobin tuntuba
Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta ce ta fitar da wasu lambobin da za a dinga tuntubar ta, ga dukkanin wani da ke da korafi kan yadda aikin Umara ke gudana a halin yanzu.
Rahotanni dai na nuni da cewa al’umma da dama ne ke zube a filin jirgin saman garin Makka da kuma Jidda wadanda kamfanoni da suka kai su suka zubar da su.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta NAHCON ta fitar a jiya Laraba ta bakin jami’ar yada labaran hukumar Fatima Usara ta ce a kokarin da hukumar ke yi na kaucewa samun matsala tuni hukumar ta aike da ma’aikatan ta zuwa kasar ta Saudiyya domin duba halin da al’umma ke ciki.
Haka kuma hukumar ta NAHCON ta bukaci dukkanin wadanda ke da korafi da su tuntubi jami’an hukumar a wurare daban daban da aka ajiye su ko kuma Jami ‘anta da ke shalkwatar hukumar ta NAHCON da ke Jiddah.
Hukumar ta NAHCON ta kuma shawara ci wadanda suka gudanar da ayyukan Umrah a bana da suyi kokari kada su ketare kwanakin da aka diba musu.