Labaran Kano
Hukumar alhazai ta Kano zata dauki mazauna Saudiya ma’aikatan wucin gadi
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce daga yanzu zata dauki ma’aikatan da zasu gudanar da aikin hajji daga cikin mazaunan Saudiya ne da ta tantancesu tare da amincewa da su.
Idan za’a iya tunawa dai a cikin wani faifan bidiyo na wata mata da ma’aikatan hukumar mazauna Saudiya da ke nuni da wani jami’a wanda ake cewa center officer na karamar hukuma da ake zargin ya damfari ta kudin guziranta a lokacin aikin hajjin bara.
Ko da hukumar alhazai ta kafa kwamitin don binciken kan al’amari har kawo yanzu babu wani bayani, hasali ma tuni aka nemi ma’aikacin aka rasa.
Sakataren hukumar alhazai Alh Muhammad Abba Dambatta a wata sanarwa da ya fitar jiya ya bayyana cewar hakan ba zata sake faruwa tuni suka samar da mafuta don magance afkuwan hakan.
Alhaji Dambatta ya ce hukumar zata kaddamar da wani asibiti na hukumar alhazan Kano karkashin kulawar hukumar alhazai ta ksa wato NAHCON.
Ya kara da cewa tana dab da fara dasa harshashen aikin gina wani gida mai dauke da gadajen alhazai kimanin dubu 500 a nan Kano.
Da yake Magana shugaban hukumar Abdullahi Saleh Pakistan ya bukaci dukkanin jami’ai da su kasance masu tsoro wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.