Labarai
Hukumar bada da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta karɓi ‘yan ƙasar guda 180 da ke makale a kasar Libya

Hukumar bada da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, tare da wasu jami’an gwamnati, sun karɓi ‘yan ƙasar guda 180 waɗanda suka maƙale a kasar Libya bayan da aka yo jigilarsu.
Jami’an sun tarba tare da karbar mutanen ne a filin jirgi na Murtala Muhammed da ke birnin Legas.
Daga cikinsu, akwai maza manya 45, da mata manya 102, da yara maza shida, da kuma yara mata 13, sai kuma jarirai maza da mata bakwai-bakwai.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa 46 daga cikin ‘yan Najeriyar da aka kwaso ba su da lafiya, abin da ya sa aka wuce da su asibiti.
Ƙungiyar kula da harkokin ‘yan gudun hijira ta duniya International Organization for Migration IOM ce ta ɗauki nauyin jiglar mutanen bisa haɗin gwiwa da hukumomin kasar.
You must be logged in to post a comment Login