Manyan Labarai
Hukumar bincike kan hadarin jiragen sama ta fitar da rahoto kan jirgin da ya fadi a Legas

Hukumar bincike game da aukuwar hadarin jiragen sama ta kasa AIB ta fitar da kwarya-kwaryar rahoton farko na hatsarin jirgi mai saukar Ungulu da ya fada kan wani gini a yankin Opebi da ke Jihar Lagos a ranar 28 ga watan Agustan jiya.
Rahoton ya bayyana cewa karewar man jirgin ce ta haddasa hatsarin.
Jirgin dai ya tashi ne daga garin Fatakwal na Jihar Rivers da karfe 9:20 na safiyar ranar, wanda ake sa ran saukarsa a Lagos da sa’o’i biyu da minti 40 bayan tashinsa, amma kuma ya fada kan wani gini da karfe 12:14 na rana.
Haka zalika binciken ya gano cewa wa’adin sakamakon gwajin lafiyar matukin jirgin ya kare tun a ranar 6 ga watan Agustan da ya gabata.
You must be logged in to post a comment Login