Labarai
Hukumar DSS ta musanta cewa jami’anta na da hannu wajen taimakawa Nnamdi Kanu wajen tserewa
Hukumar tsaron sirri ta DSS ta musanta cewa wasu jami’anta guda biyar suna da hannu wajen taimakawa shugaban ‘yan awaren Biafra ta IPOB Nnamdi Kanu tserewa daga gidansa da ke garin Umuahia a jihar Abia a ranar 14 ga watan Satumban shekarar da ta gabata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar Peter Afunanya.
Sanarwar ta ce labaran da yak e bayyana cewa wasu jami’in hukumar biyar ne suka tallafawa Nnamdi Kanu tserewa shifcin gizo ne kawai.
Hukumar ta DSS ta kuma bayyana cewa manufar wadanda suka yada farfagandan shine domin bata sunan hukumar.
Mr. Peter Afunanya ya kara da cewa masu yada farfagandan suna kuma yunkurin kawo matsala ga babban zaben kasa wanda za ayi a shekarar badi.