Kiwon Lafiya
Hukumar EFCC ta gano tsabar kudi fiye da naira biliyan 2 da miliyan 400 a gidan tsohon babban hafsan saman kasarnan
Wani shaida a karar da hukumar EFCC ta shigar gaban babbar kotun tarayya da ke Ikoyin Jihar Lagos Tosin Owobo, ya shaidawa Kotun cewa an gano tsabar kudi Naira biliyan 2 da miliyan 400 da Dala Miliyan 115 da gidaje 12 har ma da wasu Motocin Silke a hannun tsohon babban Hafsan Saman kasar nan Air Marshal Adeola Amosu mai ritaya.
Air Marshal Amosu na fuskantar tuhuma tare da wasu manyan jami’an Sojin Air Vice Marshal Jacob Adigun da Air Commodore Gbadebo Olugbenga.
Sauran wadanda ake zargin akwai kamfanoni 7 da su ka hadar da Delfina Oil and Gas Limited da McAllan Oil and Gas Limited, Hebron Housing and Properties Company Limited, sai Trapezites BDC.
Akwai Fonds and Pricey limited, Deegee Oil and Gas Limited da Timsegg Investment Limited da kuma Solomon Health Care Limited.
Sai dai Lauya mai kariya Bolaji Ayorinde ya musanta duk zarge-zaregen, inda kuma Alkalin kotun ya dage zaman Shari’ar har zuwa ranar 18 ga watan Afrilun gobe domin ci gaban Shari’ar.