Kiwon Lafiya
Hukumar EFCC tayi wa tsohuwar ministan sufurin jiragen sama tambayoyi
Jami’an Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa sun yi wa tsohuwar Ministar Sufurin jiragen saman kasar nan Stella Oduah tambayoyi bayan gurfana da ta yi a Ofishin hukumar a jiya.
Stella Oduah ta shafe tsawon Sa’o’i takwas tana amsa tambayoyi kan wani kwantiragin sama da Naira Biliyan 9 da ta baiwa wani Kamfani domin samar da kayayyakin tsaro a Filayen Jiragen sama 22 a fadin kasar nan.
Wakilan wani kamfanin kasar Amurka da EFCC ta gayyata domin bada ba’asi, ya shaida cewa Misis Stella Oduah ta kwace kwangilar dag hannunsu sannan ta mikawa wani kamfani da take da alaka da shi.
Rahotanni sun nuna cewa EFCC ta aikewa Stella Oduah takardar gayyata tun a ranar 13 ga watan Yunin bara amma ta ki mutunta gayyatar har sai da ta ji labarin suna kokarin ayyana ta a matsayin wadda suke nema ruwa a jallo, sannan ta gurfana a jiya.
Stella Oduah dai ita ce ’yar Majalisar Dattijai mai wakiltar Anambra ta Arewa.