Labarai
Hukumar EFCC zata gurfanar da tsohon gwamnan Kano bisa laifin halatta kudaden haramun
A yau ne a ke sa ran hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati zata gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau a gaban babbar kotun tarayya da ke nan Kano bisa laifin halatta kudaden haramun.
Rahotanni na nuni da cewa tun a daren jiya ne dai Hukumar ta EFCC ta tsare Malam Ibrahim Shekarau da kuma tsohon ministan harkokin kasashen ketare Aminu Wali da kuma wani kwamishina a nan jihar Kano Ahmed Mansur.
Wata majiya mai karfi a ofishin hukumar ta EFCC a nan Kano ta shaidawa manema labarai cewar wadanda ake tuhumar sun shiga hannun hukumar ne da misalin karfe 9 30 na daren jiya Laraba.
Rahotannin sunyi nuni da cewa hayaniya ta kaure a kofar shiga hukumar ta EFCC lokacin da magoya bayan tsohon gwamnan suka yi yunkurin hana shigar da shi ofishin hukumar ta EFCC a daren jiyan.
Dubban magoya bayan tsohon gwamnan ne dai suka mamaye titinan da ke sansanin alhazai da ke nan kano, da wasu titinan da ke kusa da hanyar domin nuna adawar su da matakin da EFCC ta dauka na damke Ibrahim shekaru din.
Haka kuma kiris ya rage masu zanga-zangar su kwace shi daga hannun jami’an tsaro, lamarin da ya sanya hukumar ta nemi taimakon karin jami’an tsaro domin shigar da shi cikin hukumar.