Kiwon Lafiya
Hukumar FRSC ta fara tantance mutum 15,000 da za ta dauka aiki
Hukumar kiyaye aukuwar haddura ta kasa FRSC ta fara aikin tantance kimanin mutane dubu 15 a mukamai daban-daban a ci-gaba da aikin tantance wadanda za ta dauka aiki, inda yanzu haka tantancewar ke guda a jihar Kaduna.
Jami’iar da ke kula da aikin tantancewar a jihar Kaduna Susan Ajenge ita ce ta bayyana hakan ga manema labarai a yau Litinin a yayin fara aikin tantancewar da zai kwashe kwanaki biyar ana gudanarwa.
Ajenge ta ce cikin mutane dubu 15 da za a tantance a jihar ta Kaduna dubu 8 daga cikin masu matsayin digiri ne da kuma babbar dploma ta kasa HND da kuma takardar kammala karatun NCA da kuma Diploma, inda kuma sauran ke dauke da kwalin sakandare zuwa kasa.
Haka zalika wasu daga cikin wadanda ake tantancewa da suka zanta da manema labarai sun bayyana cewa aikin tantancewar na tafiya yadda ya kamata ba tare da samun wata matsala.
Hukumar ta FRSC dai ta fara aikin tantance ma’aikatan ne da ga yau Litinin a duka fadin kasar nan kuma ana sa ran za a daki kwanaki biyar ana gudanarwa.