Connect with us

Labarai

Hukumar FRSC ta yi wa manyan jami’anta 162 sauyin wuraren aiki

Published

on

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC ta amince da sauya wurin aiki ga manyan jami’anta 162 a wani babban sauyi da aka yi a manyan mukaman hukumar.

Hukumar ta bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da mataimakin kwamandanta mai kula da harkokin gudanarwa, Agboola Olundegun, ya fitar yau Alhamis a Abuja.

sanarwar, ta ruwaito cewa, shugaban hukumar Malam Shehu Mohammed, ne ya amince da wadannan sauye-sauye, inda ya bayyana cewa an yi hakan ne domin karfafa ayyuka da kuma inganta ayyukan hukumar na kare afkuwar haduna a fadin kasar nan.

Haka kuma, ya kara da cewa, wannan tsarin ya hada da nadin sabbin kwamandojin yankuna guda hudu da kuma sauya wurin aiki ga kwamandojin sassa zuwa wasu jihohi da sassan da dama

Shugaban hukumar ya kuma amince da nadin sabon shugaban sashen wayar da kan jama’a, inda aka daga mukamin tsohon mataimakin shugaban sashen, Osondu Ohaeri, domin jagorantar harkokin sadarwa da fadakar da jama’a na hukumar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!