Labarai
Hukumar gidajen gyran hali ta Kano ta musanta zargin yin lalata da matasa

Hukumar kula da gidajen gyran hali da tarbiya ta Najeriya shiyyar Kano, ta musanta wani rahoto da ya bayyana cewa ana yin lalata da matasan da ke tsare a gidan gyran hali na Goron Dutse kamar yadda wani matashi ya bayyana.
A makon da ya gabata ne matashi wanda ya ce ya zauna a gidan gyaran halin na Goron Dutse mai suna Shehu Adamu ya zargi hukumar gidan da yin sakacin da ya janyo ake yin lalata da daurarrun.
Sai dai ta cikin wata sanarwa da ya fitar kan batun, jami’in hulda da jama’a na hukumar lura da gidajen gyran hali na Kano DSC Musbahu Lawal Kofar Nasarawa, ya karyata maganganun matasan.
DSC Musbahu Lawal, ya kara da cewa hukumar gidan gyaran halin ta Kano za ta dauki matakin shari’a a kan matashin.
You must be logged in to post a comment Login