Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar gudanarwar customs ta yi karin girma ga manyan jami’an ta 1997

Published

on

Hukumar gudanarwar hukumar kwastam ta yi karin girma ga wasu manyan jami’an hukumar 1997.

Haka kuma ta kuma amince wasu manyan jami’an na kwastam hudu su kasance cikin hukumar gudanarwar.

Karin girma ga manyan jam’ian ya faru ne yayin wani taro da hukumar gudanarwar ta gudanar wadda shugaban ta ministan kudi Kemi Adeosun ta jagoranta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Mr Joseph Attah ya fitar jiya a Abuja.

A cewar sanarwar, karin girmar ya fara aiki ne tun a ranar daya ga watan Janairun shekarar da ta wuce.

Wasu daga cikin manyan jami’an hukumar ta kwastam da aka yi wa karin girmar sun hada da: DCS Talatu Isa Mairo da ACG Ibrahim Yakubu Maikarfi da ACG Ali Bukari Ama Amajam da kuma Comptroller Adesanmi Omiye.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,481 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!