Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar shirya jarabawar WAEC za ta gudanar da jarabawar GCE zagaye na 2

Published

on

Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandire ta yammacin Afirka WAEC, ta ce; nan ba da dadewa ba, za ta gudanar da jarabawar GCE zagaye na 2.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar Demianus Ojijeogu.

Sanarwar ta ce, za a fara yin rajista a yau Litinin sha hudu ga watan Mayu a kuma kammala a shida ga watan Yuli.

Demianus Ojijieogu, ta cikin sanarwar dai ya ce, daliban da basu samu damar yin rajista ba har aka rufe websites din hukumar sannan su ka dawo daga bisani suka bukaci rubuta jarabawar, idan har sun iya yin rajista awanni ashirin da hudu kafin fara jarabawar za a kyalesu su rubuta, sai dai za su biya naira dubu ashirin da biyar.

Haka zalika sanarwar ta kuma ce, suma wadanda ke da tawaya a jikinsu za su iya yin rajistar jarabawar sai dai wajibi ne su bayyana nau’in nakasa da suke dauke da ita.

Hukumar ta WAEC ta cikin sanarwar dai, ta ce; masu sha’awar rubuta jarabwar za su biya jimillan naira dubu goma sha uku da dari tara da hamsin da kuma wani naira dari biyar lada ga bankuna da sauran masu hannu wajen shirya jarabawar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!