Labarai
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama wasu matasa ‘yan daudu 7

Hukumar Hisba ta Jihar kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta cafke wasu ‘yan daudu da suke zama a yankin zoo road da ke karamar hukumar Birni bayan korafe korafen da aka yi ta kawo wa hukumar akan su.
Babban kwamandan hukumar Sheikh Mujahideen Aminudeen ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radio.
Ya kuma kara da cewa sun kama mutum sama da 7 wadanda kananan yara ne da basu wuce shekara 17 ba da suka fito daga jihohi daban daban.
Dakata Mujahideen ya kuma ce za su cigaba da gudanar da bincike domin daukar mataki na gaba, kan wadanda suka kama.
You must be logged in to post a comment Login