Labarai
Hukumar Hisbah ta kama mabarata anan Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutum 10 da ake zargin mabarata ne tun a watan Satumbar da ya kare bayan da aka yi zargin cewar sun take dokokin hukumar na yin bara akan Titunan jihar nan.
Kakakin hukumar ta Hisba Lawan Ibrahim ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sa wadanda ake zargin sun hada da maza 3 da mata 7.
An dai kama wadanda ake zargin da yin barar a tituna daban-daban a wani samame da hukumar ta gudanar a cikin birnin Kano.
Haka zalika an kama mabaratan ne akan Titunan da suka hada da Railway da State Road da dai sauran su.
Sai dai kakakin hukumar ta Hisbah ya ce bayan an tantance su daga bisani an sake su, da aka gano cewar sababbi ne wajen yin barar.
Rahotanni sun bayyana cewar an sami ragowar mabarata akan tituna tun bayan da hukumar ta Hisbah ta kaddamar da samame tare da kama su, don hana masu yin bara a jihar Kano