Labarai
Hukumar ICPC ta kwato kayayyakin aiki na naira miliyan 117 a hannun dan majalisar tarayya
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu ta kasa ICPC ta tabbatar da kwato wasu kayayyakin aiki da kimarsu ta kai sama da naira miliyan 117 a hannun dan majalisar tarayya mai wakiltar Enugu ta arewa Sanata Chukwuka Utazi, na aikin mazabu wato Constituency project.
ICPC ta ta ce ta samu kayan boye a gidan Sanata Utazi, wadanda suka hadar da Babura 60 da na’urar transformer 5 injinan nika 203 da kuma baburan adaidaita sahu guda 219.
Sanata Chukwuka Utazi wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na majalisar dattijai, ya ce ya kuduri aniyar raba kayayyakin ne ga al’ummar mazabarsa da zarar majalisar ta tafi hutunta na shekara.
ICPC ta kara da cewa tun a cikin watan Janairun bara ne aka bayar da kwangilar raba kayyakin, a matsayin guda daga cikin ayyukan mazabu na dan majaisar.
Jami’ar yada labarai ta ICPC Rashidat Okoduwa ta bayyana cewa gano kayayyakin na cikin kudurin hukumar na ci gaba da bankado duk wasu ayyuka ba a kammala ba, ko kuma wadanda ak zargin akwai almundahana a ciki.