Labarai
Hukumar Immigration ta karrama sarkin Rano
Maimartaba Sarkin Rano Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa ya yi kira ga masu hannu da shuni da masu riƙe da muƙamai da su riƙa taimaka wa al’umma domin hakan zai ƙara ƙaunar juna a tsakani.
Sarkin Rano ya yi wannan kira ne a taron karrama shi, da jami’an hukumar lura da shige da fice ta ƙasa ƴan asalin masarautar Rano bisa jagorancin tsohon shugaban riƙon hukumar Alhaji Usman Umar Dagacin Kibiya suka shirya masa a fadarsa.
A yayin taron da aka gabatar yau Asabar sarkin ya yi godiya ga Allah bisa karramawar da ma’aikatan suka yi masa, tare da addu’ar samun rahama ga tsohon sarkin Rano Ambasada Tafida Abubakar Ila.
A nasa ɓangaren Dagacin Kibiya Alhaji Usman Umar ya nuna farin cikinsa da ya kasance shi ne silar ɗaukar sarkin Rano Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa da shugaban hukumar na yanzu Muhammad Babandede aiki a hukumar.
Da yake jawabi shugaban hukumar Muhammad Babandede ya ja hankalin masu riƙe da madafun iko kan su riƙa waiwayar garuruwansu saboda hakan shi ne abu mafi dace cewa.
Wakiliyarmu Aisha Shehu Kabara ta rawaito cewar taron karrama sarkin Ranon ya sami halartar shugabannin hukumar na jihohin Kano da Jigawa da sauran jihohi, har ma da shugabanin ƙananan hukumomin Rano da Kibiya.
You must be logged in to post a comment Login