Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar INEC ta ce hukumar zaben jihar Kano bata yi amfani da rijistar ta ba a zaben kananan hukumomi da ya gabata

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bayyana cewa hukumar zabe ta jihar Kano KANSIEC da ta shirya zaben kananan hukumomi da aka gudanar a watan Fabrairun da ya gabata har ya jawo cece-kuce, ba’a yi cikakken amfani da rajistar zaben hukumar ta INEC ba.

Shugaban Hukumar zaben ta kasa INEC Farfesa Mahmoud Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja a Juma’ar nan.

A watan Maris din da ya gabata ne hukumar ta INEC ta kaddamar da wani kwamiti, da zai yi bincike kan zargin da ake yi cewa kananan yara sun kada kuri’a a yayin zaben wanda ya baiwa jam’iyyar APC damar lashe duka kujeru 44 na kananan hukumomin jihar nan.

An dai kaddamar da kwamitin ne bayan bayyana wasu hotuna a shafukan sada zumunta da ke nuna kananan yara na kada kuri’a a yayin zaben, abin da ya jawo hankalin al’umma da jam’iyya mai hammaya ta PDP cewa ba’a gudanar da sahihin zabe ba.

Yakubu ya kuma kara da cewa rahoton binciken ya tabbatar da cewa mafi yawancin rumfunan zaben ba’a yi amfani da rajistar zaben hukumar INEC ta kasa ba.

Sai dai da ya ke jawabi kan batun kada kuri’ar kananan yara a yayin zaben, Yakubu ya ce mafi yawancin hotunan tsoffafi ne, kuma ba su da wata alaka da zaben.

Sai dai kuma ya ce hukumar bata da ikon bincike sahihancin zaben kananan hukumomin ko akasin haka.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!