Kiwon Lafiya
Hukumar INEC ta ce tana ajiye da katin zabe kusan miliyan 8
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce a halin yanzu tana ajiye da katin zabe na dindindin akalla kusan miliyan 8 da ba a karba a Ofisoshinta daban-daban da ke fadin kasar nan.
Wannan na cikin rahoton da hukumar ta fitar a jiya Talata a Abuja, inda ta ayyana Lagos a matsayin Jihar da ke kan gaba wajen gaza karbar katunan na su na zabe na dindindin, inda INEC ta ke ajiye da katunanta sama da miliyan da dubu dari hudu.
Jihar Oyo ce ke biye ma ta da katunan zaben sama da dubu dari shida sai Edo da katunan zaben sama da dubu dari hudu, yayin da Jihar Kano ke da ajiyayyun katunan zaben a INEC guda dubu dari da casa’in biyar da dari tara da 41.
INEC din ta ce Jihar Anambra ce kan gaba wajen karbar katin bayan da ta karbi katuna sama da dubu dari daga bara zuwa bana sai Jihohin Lagos da Kogi suka mara mata baya.
Yayin da Jihar Zamfara ta kasance Jihar da ta karbi katunan mafiya karanci wato guda arba’in daga shekarar da ta gabata zuwa shekarar da mu ke ciki.