Labarai
Hukumar INEC ta ce zaben gwamna na jihar Kano bai kammala ba
Hukumar zabe ta kasa a nan Kano ta sanar da sakamakon gwamnan jihar Kano a matsayin wanda bai kammala ba.
A cikin daren jiya ne dai baturen zaben jihar Kano Farfesa Bello Shehu ya sanar da sakamakon zaben a matsayin wanda bai kammalaba.
A cewar farfesan ya ayyana zaben ne a matsayin wanda bai kammala, saboda adadin kuri’un da aka soke sun fi wadanda aka ci zaben da su yawa .
Da ya ke sanar da sakamakon zaben farfesan ya ce Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u miliyan daya da dubu goma sha hudu da dari hudu da saba’in da hudu, inda kuma Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri’u dubu dari tara da tamanin da bakwai da dari takwas da sha tara.
Yace adadin kuri’un da aka soke a kananan hukumomi 22 ciki har da mazabar Gama ya kai kuri’u dubu dari da arba’in da daya da dari shida da casa’in da hudu. A don haka ne baturen zaben ya ce bisa tsarin doka dole ne a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba