Labarai
Hukumar INEC ta dage zaben gwamnoni dana ‘yan majalisun jihohi da mako guda
Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da mako guda, inda ta mayar da shi zuwa 18 ga watan Maris.
Hukumar ta INEC ta sanar da hakan ne jim kadan bayan wani taron sirri da manyan jami’an hukumar ta gudanar a Abuja.
Hukumar ta INEC ta ce ‘ dalilin da ya sanya ta dage Zaɓe shine rashin kammala saita na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS, wadda aka yi amfani da ita a yayin zaɓen shugaban ƙasa, da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabirairu.
‘Ta ce dalilin samun tsaikon na saita na’urar kuwa shine biyo bayan bukatun wasu jam’iyun siyasar ga INEC din na a basu dama su duba na’u’rar BVAS din, don tabbatar da ingancin zaben daya gudana’.
‘Hakan ce ta sanya hukumar dole ta dage zaben domin tana bukatar lokacin da zata sai-saita wannan na’u’rar, don amfani da ita a zaben gwamnoni, wanda a yanzu lokacin daya rage ba zai isheta ta saita na’u’rar ba’.
Haka zalika hukumar ta ce ‘sai ta samu damar kwashe bayanan ta da ta tattara a yayin zaɓen shugaban ƙasar zuwa wani rumbunta na daban, kafin ta sake saita na’urar ta yadda za a yi zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ba tare da wata damuwa ba.
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login