Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zaben Alhassan Ado Doguwa bai kammalu ba- INEC

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC, ta bayyana zaben dan majalisar tarayya na mazabar Doguwa da Tudunwada a matsayin wanda bai kammalu ba.

Hukumar ta bayyana hakan ne a yau Laraba soke zaben ne sabo da an samu akwatuna 13 da aka soke inda kuri’un su suka kai 6,917.

Tun a baya dai jam’iyyar APC na da kuri’a 39,732 yayin da NNPP ke rufa mata baya da guda 34,718

wanda alkaluman ke nuni da cewa, kuri’un da aka soke din sun fi wadanda APC ta bai wa NNPP tazara.

Bisa haka ne Baturan zaben kananan hukumomin Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya bayyana sakamakon zaben a matsayin wanda bai kammalu ba.

Haka kuma Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya ce, za a sake zabe tsakanin NNPP da APC a Mazabu 13 da aka soke.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!