Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar JAMB ta sanar da ranar sake rubuta jarrabawar ga dalibai fiye 12,000

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan Makarantun kasar nan ta JAMB ta sanar da ranar Lahadi mai zuwa 26 ga watan da mu ke ciki na Mayu domin sake rubuta jarrabawar da dalibai fiye da 12,000 za su yi a fadin kasar nan.

Babban jami’in yada labaran hukumar Dokta Fabian Benjamin ne ya sanar da hakana Abuja lokacin da yake tattaunawa da ‘yan-jarida, inda ya ce wadanda za su rubuta jarrabawar su ne wadanda na’ura ta yi tutsu yayin jarrabawar cikin watan Maris din da ya gabata.

Har ila yau daliban da sakamakonsu bai fito ba alhalin ba a kamasu da wani laifi na aikata magudin jarrabawa ba da ma wadanda suka gaza fitar da Silif dinsu a shafin Intanet, su ma za su sake rubuta jarrabawar.

Dokta Fabian Benjamin ya bukaci daliban da za su rubuta wannan jarabawar da su garzaya shafin hukumar na Intanet domin fitar da Slif dinsu daga yau Litinin 21 ga watan Mayun da mu ke ciki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!