Kiwon Lafiya
Hukumar JAMB zata janye amfani da dangwalen yatsa
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB ta ce ba zata janye yin amfani da dangwalen yatsa ba wajen tantance masu zana jarrabawar a bana.
Hukumar ta sanar da hakan ne cikin rubutun da ta ke fitar wa duk mako da ya shafi al’amuran hukumar aka rabawa manema labarai jiya lahadi a birnin tarayya Abuja.
A cewar hukumar ta JAMB, tantance dalibi ta hanyar amfani da dangwalen yatsa ita ce hanya daya da za ta baiwa dalibi damar rubuta jarrabawar, kuma shi ne zai ba su damar shiga cibiyoyin da za a zana jarrabawar a fasdin kasar nan.
Hukumar ta ce ba za ta samar da wata rijistar tantance daliban ba, a cewar ta wannan dangwalen yatsan shi ne hanya daya tilo da za ta yi amfani da shi wajen tantance dalibanta. A don hakan ta bukaci dukkanin jami’anta da sauran masu ruwa da tsaki a harkar da su tabbatar sun bada hadin kai wajen cimma wannan nasara domin ciyar da bangaren ilimi gaba a kasar nan