Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar jin dadin Alhazai ta musanta barkewar Amai da Gudawa ga Alhazan Kano

Published

on

Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Kano, ta musanta labarin da ake yadawa cewar cutar Amai da Gudawa ta barke a tsakanin Alhazan jihar.

Darakta janar na hukumar Alhaji Lamin Rabiu ne ya musanta barkewar annobar a zantawarsa da Freedom Radio.

Ya ce, abinda suka sani dai shi ne, mahajjata mutum Tara ne suka gamu da matsalar gurbacewar ciki da ta haifar musu da Amai da gudawa bayan cin wani Dambu mara inganci.

Shi ma a nasa bangaren, jagoran tawagar likitocin da ke kula da Alhazai a kasa mai tsarki Dakta Usman Shu’aibu Galadima, ya musanta zargin barkewar cutar ta Amai da Gudawa ga Alhazan Kano.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Tukuntawa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!