Labarai
Hukumar kididiga ta kasata ce mutane miliyan 16 ne marasa aikin yi a Nijeriya
Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce mutane miliyan goma sha shida ne ba su da aikin yi a kasar nan cikin watanni hudu na karshen shekarar da ta gabata.
Hakan na kunshe ne cikin wani kundin rahoton zangon karshe a shekarar dubu biyu da sha bakwai wanda hukumar ta fitar jiya a shafinta na website kan kididdigar masu aikin yi da marasa aikinyi.
Ta cikin rahoton dai hukumar ta kuma ce akwai wasu mutum miliyan takwas da rabi wadanda su ke aikin da bai wuce akalla awa guda da kuma wasu miliyan bakwai da rabi wadanda basu aikin komai.
Haka zalika rahoton ya kuma bayyana cewa akwai wasu ‘yan Najeriya miliyan goma sha takwas da dubu dari biyu wadanda ke ‘yan kwarya-kwaryar aiki da ba su wuce awanni ashirin zuwa talatin da tara ba a sati.
A cewar rahoton na NBS al’ummar kasar nan da su ka yi aiki da ya kama daga awanni arba’in zuwa sama a watanni hudun karshen shekarar da ta wuce, sun kai sama da miliyan hamsin da daya wanda ya nuna cewa adadin al’ummar kasar nan miliyan saba’in da bakwai kenan suke da aiki a karshen shekarar da ta gabata.