Labarai
Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗɗura Ta Ja Kunnen Direbobi kan Overload
Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura ta ƙasa reshen kano ta buƙaci darebobi da su ƙaucewa gudun wace sa’a da yin lodin da bai kamata ba musamman a wannan lokaci na ƙarshen shekara kasancewar mutane nayin tafiye-tafiye domin kulawa da rayukan al’umma
Shugaban kula da yankin Kaduna Co kwamanda Umar Ahmad ne ya bayyana hakan a yau yayin taron ƙaddamar da tsarin da zai sanya ido akan direbobi da tituna domin kaucewa afkuwar haɗɗura
Co kwamanda Umar Ahmad ya ƙara da cewa wannan saƙon ya isa ga direbobi ganin yadda suka halarci taron
Da yake jawabi Kwamishinan sufuri Alhaji Muhammad Digol ya ce yana da matukar muhimmanci ga direbobi su mayar da hankali wajen kulawa da lafiyar al’umma
Yayin taron ya sami halartar nau’i daban daban na jami’ar tsaro da direbobi inda aka tattauna kan yadda za’a ƙauracewa tukin ganganci da daukan kayan da basu kamata ba
You must be logged in to post a comment Login