Connect with us

Labaran Wasanni

Hukumar kwallon Afirka CAF ta dakatar da wasan Guinea da Morocco

Published

on

Hukumar Kwallon kafa ta Afirka CAF, ta dakatar da wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin Duniya , na 2022 tsakanin kasar Morocco da kasar Guinea.

Wasan wanda za’a fafata shi a Litinin 6 ga Satumba 2021, an dage shi sakamakon juyin Mulkin da Soji su ka yi a kasar ta Guinea.

Ya kamata ‘yan jarida su samu yancin kawo rahoton wasanni ba tare da fargaba ba – CAF

A takardar sanarwar da hukumomin CAF da ta Duniya FIFA, suka fitar sun Alakanta dage wasan da rashin tsaro da za’a iya fuskanta biyo bayan juyin mulkin.

Hukumar ta FIFA da CAF , sun ce za’a sake saka ranar da za’a fafata wasan ,a cikin kasar ko a wata makociya da zarar an samu kwanciyar hankali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!