Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

An kammala gasar fitar da gwanaye ta jihohin Arewa maso Yamma a Najeriya

Published

on

Biyo bayan kammala wasannin cancatar shiga gasar matasa ta kasa ‘National Youth game ‘ ta Matasa ‘yan kasa da shekaru 15, daga  jihohin   shiyyar Arewa maso Yamma.

Jihar Kano ta kare a mataki na 3, yayin da tawagogin ta 3 suka samu damar shiga gasar ta kasa da za ta gudana a watan Oktoba mai zuwa.

FC Galadima na Zawarcin Dan wasan Diamond Star Aliyu Haidar

Gasar wacce jihohi 7, daga yankin da suka hada da Kano, Kaduna , Kebbi, Katsina , Jigawa , Sokoto da Zamfara ne za su halarci gasar, Amma Biyar ne suka je saboda Zamfara da Jigawa Basu halarta ba.

Kungiyar Zari Ruga ta Rugby, Maza da Mata, tare da ta Kwallon Kwando wato Basketball itama Maza da Mata, sai ta Kwallon Volleyball ta Maza, daga Kano za su wakilci jihar a wasan na kasa da zai gudana a Ilorin ta jihar Kwara.

Tawagar Kano, ta Kwallon kafa Bata samu tikitin zuwa gasar ba , Bayan da aka doke ta a semi final daci 5-3, jihar Kebbi Kuma ita ta samu tikitin zuwa gasar kasa , Bayan da ta doke Kaduna a wasan karshe da ci 2-1.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!