Labarai
Hukumar Kwastam ta cafke Wiwi da haramtattun kaya na miliyoyin kudi

Hukumar hana fasakauri ta Najeriya Kwastam ta ce, jami’anta sun kama tabar wiwi da kudinta ya kai naira miliyan 48 da dubu dari 5 da wasu kayan da aka haramta shigo da su na naira miliyan 220 a Jihar Kaduna.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito an kama kayayyakin ne a ayyuka daban-daban da jami’an hukumar suka gabatar.
Hukumar ta kwastam ta ce an miƙa wanda ake zargin da kayan ga jami’an hukumar yaki da ƙwayoyi ta kasa NDLEA don ci gaba da bincike da gurfanarwa a gaban shari’a bisa tsarin haɗin gwiwar hukumomi.
You must be logged in to post a comment Login