Labarai
Annobar Ebola ta tilasta hana taron Jana’iza a Congo

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce haɗarin yaɗuwar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ya ƙaru matuƙa, sai dai ta ce babu barazana sosai kan yaɗuwar cutar a duniya.
Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce akwai bukatar a samu yarda da aminci tsakanin ma’aikatan lafiya da alummomi domin hakan zai taimaka wajen shawo kan cutar.
Hukumomi a lardin Ituri, inda cutar ta fi shafa sun haramta taron jana’iza da zaman makoki.
Hakan na zuwa ne bayan da wasu fusatattun ƴan’uwan wani mamaci suka cinna wa asibiti wuta bayan da jami’an lafiya suka ki ba su gawar ɗan’uwansu, saboda tsoron yaduwar cutar.
WHO ta ce tana tunanin mutum aƙalla 750 sun kamu da Ebola, yayin da aƙalla mutum 177 suka mutu.
You must be logged in to post a comment Login