Connect with us

Labarai

MDD ta ce jami’an lafiya 70 ne suka gamu da cutar Ebola a Congo kuma 17 sun rasa ransu

Published

on

 

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla jami’an lafiya 70 ne suka gamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, kuma cikinsu 17 sun rasa ransu.

 

Wannan adadi ya fara ne tun lokacin da cutar ta barke a ƙasar kusan watanni biyu da suka gabata.

 

Bincike ya nuna cewa cutar ta jima tana yaɗuwa kafin mahukunta su sanar da ɓullarta a hukumance, abinda ke nufin jami’an lafiya sun yi mu’amala da masu cutar ba tare da cikakkiyar kariya ba.

 

Ko a yanzu da aka tabbatar da cewa cutar ta zama annoba a ƙasar jami’an lafiya na kokawa game da ƙarancin kayan kariya daga cutar da kuma sinadaran kashe ƙwayoyinta.

 

Congo na cikin ƙasashen Duniya da ke fama da ƙarancin jami’an lafiya da kayan aikinsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!