Kiwon Lafiya
Hukumar NABTEB ta sanar da dakatar da magatakardar hukumar
Hukumar shirya jarrabawar kammala Makarantun Sakandaren Fasaha da Kasuwanci ta kasa NABTEB ta sanar da dakatar da Magatakardar hukumar Ifeoma Abanihe tare da wasu daraktoci 4 daga aiki sakamakon zargin almundahanar kwantiragi da kudinsu ya kai Naira Miliyan 49.
Sanarwar dakatarwar dai na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da sa-hannun shugaban hukumar gudanar NABTEB Farfesa Shilgba, wanda ya ce hukuncin ya biyo bayan karbar rahoton binciken da suka karba ranar 21 ga wannan wata na Yuni, karkashin jagorancin Dokta Charles Imori.
Baya ga Maga-takardar akwai wasu Daraktoci 4 da dakatarwar ta shafa da suka hadar da Daraktan kudi da kididdiga da takwarorinsu na jarrabawa da gudanarwa da na jarrabawa da ci gaba sai kuma na bangaren cinikayya.
Dakatarwar ta biyo bayan kammala taron hukumar gudanarwar a garin Benin na Jihar Edoa ranar 19 ga watan Yunin nan da muke ciki, inda suka gano cewa suna da hannu cikin badakalar kudi Naira Miliyan 49.
Tuni dai Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya amince da wannan hukunci, tare da shirin matakin da za a dauka na gaba.